Ina Makomar Masu Yada Labaran Karya A Lahira?

Daga Laraba

Daga Laraba
Ina Makomar Masu Yada Labaran Karya A Lahira?
Mar 23, 2022
Aminiya

Makonni biyar ke nan da shirin Daga Laraba ya fara fede biri har wutsiya kan batun labaran karya domin gano asalinsa da masu amfana da shi da masu yadawa da kuma amfanin da su ke samu.

Yadda Ake Gane Labaran Karya ne batun da shirin Daga Laraba na makon da ya gabata ya mayar da hankali a kai.

A wannan makon kuma shirin ya karkata ne kan  Irin Kallon Da Addini Ke Yi Wa Labarin Karya.

Mun tattauna da malaman addinin Islama da na Kirista domin sanin makomar masu yada shi a wurin ubangiji.