Anya Akwai Ranar Da Za A Wayi Gari Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Zama Tarihi A Najeriya?

Daga Laraba

Daga Laraba
Anya Akwai Ranar Da Za A Wayi Gari Ta'addancin 'Yan Bindiga Ya Zama Tarihi A Najeriya?
May 04, 2022
Aminiya

Ta'addancin 'yan bindiga ya zamo ruwan dare a Najeriya. Domin babu nau'in da ba a gwada irinsa a kasar nan ba. 

Anya akwai ranar da wannan ta'addanci zai zamo tarihi kuwa?

Mene ne ya kamata ayi domin a gaggauta kawo karshen ta'addanci, wane ne ya kamata a sa a gaba domin neman mafita, mene ne ake yi daidai kuma mene  ne ake bukatar a gyara?

Mazauna yankunan da 'yan ta'adda ke ciwa tuwo a kwarya sun yi mana bayanan halin da suke ciki da kuma tunaninsu dangane da yiwuwar kawo karshen ta'addanci. 
Mun kuma ji ta bakin masana harkokin tsaro domin sanin nasu hasashen kan karshen ta'addanci a Najeriya.