A cigaba da ayyukan 'yan ta'addan IPOB a Kudu maso Kudancin Najeriya, yan kungiyar sun kai farmaki yankunan da Hausawa ke zaune inda suka hallaka wata mata mai dauke da cikin wata tara da 'ya'yan ta hudu a Isolo dake Jihar Anambra.
Bayan nan rahotanni da muka samu sun nuna cewa a kasa da awa 24 bayan kashe matar nan da 'ya'yanta, yan haramtacciyar kungiyar sun sake kashe wasu yan acaba 4 sun kuma kone gawar daya daga cikin su, sannan kuma sun kashe wani mahauci.
Ko wane hali 'yan Arewa mazauna yanki ke ciki a yanzu?
Muna tafe da bayanan yadda aka kashe mata mai cikin nan da kuma karin bayani kan halin da 'yan Arewa mazauna yankin ke ciki a halin yanzu.