Rahotanni kan halinda makarantu da karatun boko ke ciki a Jihar Bauchi na cigaba da janyo takaddama a tsakanin jama'a. Biyo bayan sabbin tsare-tasren da gwamnatin jihar ta kawo.
Wadanne tsare-tsare ne wadannan da jama'a ke tattaunawa akansu, kuma ta wadanne hanyoyi suka shafi rayuwar jama'a.
Shirin Daga Laraba na wanna mako ya yada zango a Jihar Bauchi domin binciko gaskiyar abinda ke faruwa.