Batun lalacewar harkar ilimi a Jihar Kebbi ba sabon labari bane a kunnuwan 'yan Najeriya, musamman batun daliban da ke jarrabawar sharar fagen shiga jami'a.
An jima ana kwarmata batun lalacewar gine-gine da rashin kwararrun malamai da kayan koyarwa a jihar, domin samar da ilimi mai inganci.
A wannan karon, shirin Daga laraba ya yada zango a bangaren ilimin Jihar Kebbi domin bankado irin badakalar da bangaren ke ciki da niyyar neman mafita.