Idan ana biye da mu, a cikin shirin Daga Laraba na makon jiya, mun tattauna ne a kan harkar ilimin jihar Sakkwato, a wannan makon kuma, mun tabo harkar ilimin jihar Zamfara ne.
Ilimi aka ce shi ne gishirin zaman duniya, amma idan ba ilimi, sai jahilci ya yi katutu.
Masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimin jihar Zamfara, sun alankanta rashin tsaro a matsayin matsala ta farko kuma babba da ke ci wa ilimi a jihar tuwo a kwarya.
Shirin Daga Laraba ya leka Jihar Zamfaran inda ya tattauna ya kuma jiyo dalilan tabarbarewar ilimin jihar.