Dalilan Da Daliban Kano Ke Yawan Faduwa Jarabawa

Daga Laraba

Daga Laraba
Dalilan Da Daliban Kano Ke Yawan Faduwa Jarabawa
Jul 20, 2022
Aminiya

Ko me ya sa harkar ilimi, musammam a Arewacin Najeriya sai kara tabarbarewa yake yi, har yana neman mutuwa?

A makonnin baya, mun kawo muku yadda harkokin ilimi ke tafiya a jihohin Bauchi, Kebbi, Sakkwato da Zamfara.

Yau ga mu a Jihar Kano, inda muka yi tankade da rairaya kan yadda dalibai ke yawan faduwa jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da kuma JAMB, wadda ake zanawa domin sharar fagen shiga jami’a.

Mun tattauna da dalibai da kuma masu ruwa da tsaki a kan wannan lamari.