’Yan Arewacin Najeriya akalla 200 ne ke tsare a hannun jami’an tsaron yankin Kudu maso Yammcin Najeriya (Amotekun), cikinsu har da fasinjoji 19 da suka shafe wata 10 a tsare.
Shin Amotekun halastacciyar kungiya ce a Najeriya kuma tana da harumin tsare ’yan kasar haka kawai?
A shirin namu na yau, za ku ji halin da ’yan Arewa da Aamotekun ta tsare suke ciki da matsayin doka a kan kungiyar da kamen da ta yi da kuma yadda za a shawo kan lamarin.