Cigaban da aka samu a bagaren sadarwar zamani ta sa abubbuwan da ake yi a zahiri yanzu an koma yin da yawa daga cikinsu ta kafafen sadarwa, ciki harda cinikayya da kuma shawarwari kan zamantakewar rayuwa da na auratayya.
Shin wadanda ke da irin wadannan shafukan kwararru ne kuwa, wace irin nasara a ke samu in an dauki shawarar, ko kuma dai barna a ke yi mai-makon gyara?
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazarin irin wadannan shafuka da irin tasirin da su ke yi wurin inganta ko lalata zamantakewa.