Wata kididdiga da jaridar Vanguard ta fitar a 2017 ta bayyana cewa akwai kabilu da ke amfani da harsuna 371 a fadin Najeriya.
Ta yaya wadannan kabilu za su fahimci junansu su zauna lafiya har su amfani kansu da kasarsu?
Saurari cikakken shirin Daga Laraba domin jin yadda masana da ’yan Najeriya suka bayyana hanyoyin da za a bi wurin cudar guna da man jikinta.