Taimakon juna na daya daga cikin hallayyar da ake kwatanta mutane masu nagarta da shi, amma a yanzu abin yana neman zama tarihi.
Shin me ya sa taimakon juna ya yi karanci a wannan zamanin?
Saurari labarin wadansu da aka zalunta a gaban jama’a amma ba a kawo musu dauki ba.
Mun kuma tattauna da masana kan yadda aka tsinci kai a halin rayuwar ba ruwan kowa da kowa.