Matsalar yawon talla ta dade tana ci wa al’ummar Arewacin Najeriya tuwo a kwarya.
Me ya sa aka fi dora wa ’yan mata talla ta kasar Hausa kuma tsakanin amfani da illolin talla wanne ne a gaba?
Shirin Daga Laraba ya dubi maganar talla da idon basira, don neman mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomi da masana a fannin ilimin addini da na duniya.