Ana sa ran a tashi da Azumin watan Ramadan mai albarka ranar Alhamis idan Allah ya yarda.
Shin kun san matakan samun nasara a cikin ibadar wannan wata?
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya tattaro bayanai da shawarwari na alheri game da yadda za a rabauta da alheran da ke cikin watan azumin Ramadan.