Rigingimu tsakanin ma'aurata dake samo asali daga zama wuri daya da iyayen miji musamman uwa na daya daga cikin matsalolin da ake fama da su a Arewacin Najeriya da ma duniya baki daya.
Tarihi ya nuna, an yi zamanin da iyaye da 'ya'ya ke zama wuri guda lafiya, mene ne ya canza da a wannan zamanin ba a iya zama wuri guda da iyaye kuma a zauna lafiya?
Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadanda abin ya shafa, ya ji ta iyayen, ya ji ta 'ya'yan, ya kuma nemi shawarwarin masana kan mafita.