Matsalar rashin zaman lafiya da tausayin juna a tsakanin ma'aurata a wannan zamani daya ne daga cikin matsalolin da ke ciwa mutane da dama tuwo a kwarya, lura da cewa, wadannan matsaloli na zama sanadiyyar mace-macen aure.
Shin ko kun san baya ga matsalolin da ke samo asali daga ma'aurata da abokan huldar su akwai sako-sako da walittaka a cikin musabbaban tabarbarewar zamantakewar ma’aurata da lalacewar aure a wannan zamani?
Binciken Shirin Daga Laraba na wannan mako ya gano sako-sako da walittaka a wannan zamani na daya daga cikin dalilan tabarbarewar zamantakewar ma’aurata da lalacewar aure a wannan zamani.