Tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 da aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya ya bayyana cewa babu tallafin mai a cikin kasafin kudin da ya gada da zai kama aiki daga 1 ga Yunin da muke ciki, saboda haka batun tallafin mai ya tafi ke nan.
Ko ta wadanne bangarori cire tallafin mai ya shafi rayuwar 'yan kasar?
Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayanai daga bakin wadan da cire tallafin mai ya shafi rayuwarsu kai tsaye, da kuma bayanan masana kan wannan batu.