Me Ya Sa Juyin Mulki A Wasu Kasashe Ya Dami Tinubu?

Daga Laraba

Daga Laraba
Me Ya Sa Juyin Mulki A Wasu Kasashe Ya Dami Tinubu?
Sep 06, 2023
Aminiya

Juyin mulkin da ake yi a ƙasashen Afrika a 'yan kwanakin nan yana tayar da hankalin shugabannin yankin, inda suke ta ƙoƙarin ganin an dawo mulkin dimokraɗiyya.

Sai dai wasu na ganin yawan tsoma baki da shugaban Najeriya Bola Tinubu ke yi, bai kamata ba musamman ƙasashen da ba su cikin yankin ECOWAS da yake jagoranta. Duk da yake akwai masu ganin girman Najeriya a Afrika ya sa dole ya yi magana.

Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari akan abin da ya sa shugaba Tinubu ke saurin tsoma baki ga ƙasashen da aka yi juyin mulki fiye da sauran shugabannin Afrika.