Tasirin goro ga masu cinsa yana zama abu mai wahala mutum iya dainawa. Goro na da mahimmanci a Kudancin Najeriya musamman ga Kabilar Igbo.
Haka ma yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa da mata a wasu lokutan suna cin goro, inda abin ya kan zame musu jiki, yayinda ake amfani da shi a wajen taruka na aure ko suna duk da ba a nomanshi a yankin.
Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba abin da ya sa masu cin goro basu iya dainawa da kuma abin da masana suka ce zai iya faruwa idan cinsa yayi yawa.