Rade-radin matsaloli basa karewa dangane da masanaantar shirya finafinai ta Arewacin Najeriya mai cibiya a Kano Kannywood.
Shin mene ne abin da ke hana Kannywood cigaba kamar sauran takwarorinta na duniya?
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi boyayyun matsalolin da suka dabaibaye Kannywood.