Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a
Daga Laraba
More Info
Daga Laraba
Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a
May 08, 2024
Aminiya

Idan aka zagaya jami’o’i ana samun dalibai da dama wadanda ba su wuce shekara 15 ba a aji. A yanzu zamani ya sauya, abin ya zama Ruwan dare.

Mai yiwuwa a lokacin da kuke makarantar firamare ko sakandare kun hadu da wadanda aka yiwa tsallaken aji, wato a bai wa dan aji 4 damar rubuta jarabawar kammala firamare ko kuma dan SS2 damar rubuta WAEC ya wuce jami’a

Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta ce za a tabbatar da dokar hana duk wanda bai kai shekara 18 ba zuwa matakin gaba da sakandare. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi duba a kan wannan lamari.