Yau Laraba rukunin farko na maniyyata Hajjin bana daga Najeriya za su tashi zuwa kasa mai tsarki
Duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, akalla mutum sama da 50,000 ne ake sa ran za su sauke faralin daga Najeriya. Shin wane abu maniyyatan ya kamata su maida hankali a kai?
Shirin Daga Laraba na wannan mako yana dauke da amsohin wadannan bayanai game maniyyata Hajjin bana.