Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi.
A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri.
Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya.