Mata na yawan ambaton kansu da zumunci a tsakaninsu har sukan bugun kirji da cewa ‘ciwon ’ya mace na ’ya mace ne.’
Amma a zahiri ko takarar siyasa mace ta tsaya, ’yan uwanta mata ke fara yaƙarta kafin maza?
Me ya sa kishi ya yi yawa a zukatan mata har ba sa iya bari mijinsu ya auro kawarsu su zama abokiyan zama? Ina ciwon ’yan macen?
Shin ko’ina haka abin yake, ko a Najeriya ne kadai?
Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya rairayo manyan dalilan da mata ke yawan samun rashin jituwa a tsakaninsu.
A yi sauraro lafiya.