Zabe na yi wu wa ne idan a kwai masu zabe, nan da watanni 13 za’a gudanar da babban zabe a Najeriya.
Shin kun san yadda zaku yanki katin zabe?
Idan kun sauya unguwa ko gari wadanne hanyoyi zaku bi wurin karbar sabon katin da zai baku damar zabe a duk inda kuke?
Shirin Daga Laraba na wannan makon ya tattaro bayanan matsalolin da a ke fuskanta wurin yankar katin zabe, da hanyoyin da za’abi wurin warwaresu a cikin sauki.