Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a rayuwar al'umma

Daga Laraba

Daga Laraba
Yadda labaran karya ke hana ruwa gudu a rayuwar al'umma
Feb 02, 2022
Aminiya

Samuwar fasahar sadarwa ta zamani ta fadada damar da mutane suke da ita ta samarwa da kuma yada labarai ta hanyoyin zamani musamman kafofin sada zumunta.

A hannu guda kuma hakan ya haifar da fantsamar labaran kanzon kurege da a wasu lokuta suke yin illa ga mutuncin jama'a har ma da tayar da zaune tsaye.

 Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado yadda aka fara samun labaran bogi, wadanda suka fi yada su da kuma hanyoyin da labaran karyan ke hana ruwa gudu a cikin al'umma.

A yi sauraro lafiya.