Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
Daga Laraba
Daga Laraba
Dalilan Da Suka Sa Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
Jan 29, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban.

A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba.
Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata?

Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar ’ya’ya maza a kan ’ya’ya mata.