Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa.
Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa.
Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba.
Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.