Boyayyun Dalilan Da Suke Sa Faduwa Jarabawa A Najeriya

Daga Laraba

Daga Laraba
Boyayyun Dalilan Da Suke Sa Faduwa Jarabawa A Najeriya
May 07, 2025
Idris Daiyab Bature

Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban.

Daya daga cikin nau’ukan jarabawa da daliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Sharen Fagen Shiga Manyan Makarantu, wato UTME.


Kamar kowace shekara, a bana ma dalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar sun samu kasa da maki 200.
Ko wadanne dalilai ne suke kawo faduwa jarabawa a Najeriya?


Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi kokarin amsawa.