Dangantaka na kara runcabewa tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, wato Kano State Censorship Board, hukumar da aka kafa a shekarar 2001 domin kula da tsaftar fina-finai da nishaɗi a jihar, musamman a fannin kiyaye al’ada da koyarwar addini wacce daya daga cikin jaruman fina finan Abba El-Mustapha, ke jagoranta.
A baya-bayan nan, hukumar ta fitar da sanarwa inda ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22. Wannan mataki ya biyo bayan saɓani tsakanin hukumar da wasu masu shirya fina-finai, inda hukumar ke zargin cewa fina-finan sun ƙetare ƙa’idoji.
Sai dai masu shirya fina finan sun bayyana cewa sam hukumar bata da hurumin dakatar da wadannan finafinai.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan rigimar da ta balle tsakanin hukumar tace fina finai ta jihar Kano da kuma masu shirya fina finai masu dogon zango.