Masana da masu sharhi suna ganin cewa rasuwar shugaba Muhammadu Buhari ta haifar da babban gibi a siyasar Najeriya, musamman a Arewa.
Wasu ma suna ganin rasuwar Buhari ka iya kawo tasgaro ga jamiyya mai Mulki, wadda take ganin shi danta ne, da ma sabuwar hadakar ’yan adawa, wadanda suke ganin yana tare da su.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan yadda siyasar Najeriya za ta kasance bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.