Takaddama ta dabaibaye batun wata matashiya mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in Department of State Services mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare da tsare ta na tsawon lokaci ba tare da sanin inda take ba.
Rahotanni sun ce ana zargin jami’in ya sauya mata addini daga Musulunci zuwa Kiristanci tare da canza mata suna zuwa Chinaza, lamarin da iyalanta suka ce an yi ba tare da yardarta ba ko kuma amincewar danginta.
Haka kuma, bayan shafe lokaci mai tsawo a hannunsa, an ce Walida ta haifi jaririya mace, abin da ya kara jawo cece-kuce da damuwa a tsakanin iyalanta da kuma al’umma, musamman dangane da zargin take mata ’yanci da kuma amfani da iko ba bisa ka’ida ba.
Lamarin ya jawo kira daga kungiyoyi da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam da su ke bukatar gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya, tare da tabbatar da adalci ga Walida da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi idan har zarge-zargen sun tabbata.
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi duba ne kan takaddamar da ta dabaibaye batun walida Abdullahi wata da ake zargin wani jami’in hukumar DSS da sacewa.