Yadda Wayar Hannu Ta Zamo Jinin Jikin Mutane A Yau
Najeriya a Yau
Najeriya a Yau
Yadda Wayar Hannu Ta Zamo Jinin Jikin Mutane A Yau
Feb 14, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Wayar salula na daya daga cikin manya-manyan abubuwan cigaban da aka samu a karni na 21 kuma ta samu tagomashi sosai ne bayan yaduwar kafofin sada zumunta.

A kan haka ne mutane kan shafe tsawon lokaci suna gudanar da harkoki daban-daban ta wayoyinsu.

Shin wadanne alfanu mutum zai samu daga yawan zama tare da wayar salula? Wadanne illoli kuma za a samu idan wayar ta zame wa mutum wani bangare na rayuwarsa?