Tun farkon satin nan ake wahalar man fetur a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da kewa, sakamakon shigowa da gurbataccen man fetur din da a ka ce anyi a satin da ya gabata.
Farsahin ababen hawa ya tashi, an kuma samu karancin ababen hawan da ya tilastawa da yawa fara tafiyar kafa.
yayinda masu sayar da mai a galan da aka fi sani da 'yan bumburutu ke cin karensu babu babbaka.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanan irin wainar da ake toyawa.