Yakin da ya barke tsakanin Ukraine da Rasha zai shafi kasashen duniya da dama, musamman wadanda su ka dogara da samun kudin shiga ta hanyar fitar da danyen mai.
a daya gefen kuma akwai yiwuwar a samu fantsamar kananan makamai cikin duniya sanadiyyar wannan yaki idan ya yi kamari.
Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanan musabbabin rikicin da kuma hanyoyin da zai shafi sauran sassan duniya.