APC A Idon 'Yan Najeriya Bayan Tara Fiye Da N20bn

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
APC A Idon 'Yan Najeriya Bayan Tara Fiye Da N20bn
May 09, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Tun bayan bayyana kudin fom din takarar jam’iyyar APC ’yan Najeriya suke zura ido domin ganin wadanda za su saya.

Rahotanni sun bayyana cewa kudaden da jam’iyyar ta tara kawo yanzu, sun sa yawancin ’yan Najeriya sun saki baki saboda mamaki, lura da yadda APC din take yawan ambatar yaki da cin hanci.

’Yan Najeriya da masu sharhi sun bayyana wa shirin Najeriya A Yau  irin kallon da suke yi wa jam’iyyar, da kuma makomar matakin jam’iyyar na sayar da fom din takararta a kan farashin da ya zarce na sauran jam’iyyu.