Yadda Sauyin Yanayi Zai Shafi Daminar Bana

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Sauyin Yanayi Zai Shafi Daminar Bana
May 10, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us Fan Mail

Alamu sun fara nuna yadda sauyin yanayi zai shafi daminar bana, bayan hasashen hukumomin Najeriya suka yi kan ruwan sama da kuma katsewarsa a farkon daminar. 

Ana ciki haka sai ga wata guguwa mai karfin gaske da ta shafi jihohin  Adamawa da Katsina a makon jiya.

Mun tattauna da Hukumar lura da yanayi ta Najeriya da kuma masanin kimiyyar noma domin jin yadda za a tunkari wadannan kalubalenen.