Najeriya a Yau

Shekara 23 Da Mulkin Dimokuradiyya; Ina Aka Kwana?

June 13, 2022 Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed
Najeriya a Yau
Shekara 23 Da Mulkin Dimokuradiyya; Ina Aka Kwana?
Show Notes

Ranar 12 ga Yuni na 2022 mulkin dimokuradiyya ke cika shekara 23 da kafuwa a Najeriya ba tare da samun wani cikas ba.

A wadannan shekaru idan an saka kasar a fai-fai, cigaba aka yi ko kuma baya, mene ne ake bukatar a gyara a tafiyar da  dimukuradiyya Najeriya.

'Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan yadda su ke kallon yanayin mulkin a Najeriya, sannan mun tuntubi masana domin sanin abinda ya kamata a gyara a tafiyar mulkin kasar.