Kimanin wata tara ke nan da 'yan Najeriya ke dan-dana kudar su saboda tsada da wahalar man fetur.
A Gwamnatance dai Naira 165 ne kudin litar man fetur, amma a halin da a ke ciki ana sayar da litar mai sama da Naira 200, a kasuwar bayan fage ma har Naira 500 litar man fetur din tana kaiwa.
Shirin ya binciko dalilinda aka kasa magance matsalar wahalar man fetur a Najeriya.