Hajjin bana ya zo da falalar haduwar tsayuwar Arfa da ranar Jumma'a.
Wadannan ranaku ne masu mahimmanci ga Musulmin duniya,
wadanda ake karfafa yin azumi da addu'o'i a cikinsu.
Za a yi Babbar Sallah a Najeriya cikin tsadar raguna,
shin anya za a ci nama kuwa a wannan sallar?
Mene ne kuma hukunce-hukuncen layya?
Shirin Najeriya a yau ya tattauna da malamai,
kuma wakilinmu a Kano ya zagaye kasuwan raguna don gano mana me yasa raguna suke tsada.