A Kasashen da suka ci gaba, da zarar ba su gamsu da shugabancin da ake masu ba,
za su mike tsaye don tuhumar shugabannin na su.
Amma ba safai 'yan Najeriya ke yin irin wannan hobbasan ba. Sun iya hadiye ko wacce irin gurbatacciyar gwamnati.
A Najeriya shugabanni suna tafiyar da harkokin mulkin kasa yadda suka ga dama, ba ruwan su da ko yan kasa na jin dadin abun da suke yi, ko kuma a’a.
Shirin Najeriya a yau, ya tattauna da 'yan Najeriya, da masu ruwa da tsaki a kan wannan al'amari.