Ana iya cewa cutar kwalara ta yi kakagida a Jihar Kano da ma wasu sassan Najeriya inda a duk shekara ake samun barkewar cutar, take kuma lakume rayuka.
Ko a kwana-kwanan nan, ma’aikatar lafiya ta jihar ta ce cutar ta kashe mutum biyar daga cikin 189 da suka kamu da ita a kananan hukumomi 20 na jihar a cikin wata shida .
Shin me ya sa ake yawan samun wannan cuta? Wai shin ina jami’an duba-gari suke, wadanda ke zagayawa unguwa-unguwa, gida-gida domin tabbatar da tsaftar muhalli don guje wa yaduwar cututtuka?
Mun tattauna da mazauna jihar Kano da kuma masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya.