Dambarwar siyasa ta sake barkewa tsakanin 'yan siyasa na Jam'iyyar PDP a jihar Kano.
Wannan rikici ya sake bayyana a fili a karshen makon nan da ya gabata.
Idan ba a manta ba daman zaman doya da manja ake yi a Babbar hammayar jam'iyar ta PDP, tsakanin bangaren Ambasada Aminu Wali da bangaren Shehu Wada Sagagi.
Shirin Najeriya a yau ya tattauna da 'yan Najeriya da masana da kuma masu ruwa da tsaki a kan wannan Batu.