Matsalar Tsaro Zai Iya Kawo Wa Zaben 2023 Cikas

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Matsalar Tsaro Zai Iya Kawo Wa Zaben 2023 Cikas
Jul 28, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Shin za a yi zabe a wasu  kauyukan karkarar kuwa a zaben 2023? 
Ta'addanci dai ya yi kakagida a jihohin Kaduna, Katsina, Neja da Zamfara.

Ganin cewa  an sami karancin yin rajistar katin zabe a wadannan yankuna, wasu kungiyoyi masu zaman kansu ne ke taimakawa wasu yankunan karkara yin rajistar katin zaben.

Shirin Najeriya a yau ya tattauna da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da kungiyoyi masu rajin kare hakkokin jama'a, da masana a kan wannan al'amari.