Sauya Shekar Shekarau: Wa Gari Zai Waya?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Sauya Shekar Shekarau: Wa Gari Zai Waya?
Aug 30, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Kasa da wata uku da sauya shekar tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP, ya sake yin tsallen batake zuwa jam’iyyar PDP.

A jiya ne tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya tabbatar da fita daga jam’iyyar NNPP ya kuma shige jam’iyyar PDP kai tsaye.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki akan wannan batu.