Fatar dabbobi da ake gyarawa ana ci da aka fi sani da ganda ko kpomo na daga cikin arzikin da Allah Ya huwace wa Najeriya, domin kuwa bayan ci a matsayin nama ana amfani da fatu da kiraga wurin yin takalma da jaka da sauransu.
Shin kun san irin asarar da masu cin ganda a matsayin nama ke janyo wa Najeriya kuwa?
Saurari cikakken shirin domin sanin yadda za a sarrafa ganda domin samun kudaden shiga baya ga ci a matsayin nama.