’Yan Najeriya sun jima suna kukan yadda ’yan siyasa ke zambatarsu da alkawuran ayyukan more rayuwa, amma daga bisani sai su karya wadannan alkawurra, su ki cikasu, su kuma sake dawowa su kara yaudarar jama’ar duk kakar zabe.
Shin me ya sa ’yan Najeriya ke fadawa tarkon irin wadannan ’yan siyasa a koyaushe?
Saurari wannan kashi na shirin Najeriya A Yau domin jin hanyoyin da za a bi domin tabbatar da duk wanda ya yi alkawari ya cika.