Kudurin Dokar Hukunta ’Yam Madigo Da Luwadi A Kasar Nijar

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Kudurin Dokar Hukunta ’Yam Madigo Da Luwadi A Kasar Nijar
Oct 24, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Kudirin yin dokar da za ta haramta auren jinsi, ko mu’amala tsakanin jinsi guda na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin jama’ar Najeriya da Nijar.

Shin mene ne dalilin yunkurin yin wannan doka a Nijar a dai-dai wannan lokaci?

Saurari yadda aka haramta auren jinsi a Najeriya da kuma yadda Nijar suka yunkuro wurin yakar wannan dabi’a.