Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
Najeriya a Yau
Najeriya a Yau
Ainihin Dalilin Ci Gaban Wahalar Mai —Masani
Nov 29, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Rige-rige da dogayen layikan ababen hawa sun ki karewa a gidajen mai sakamakon wahalar samun mai da ta ki ci, ta ki cinyewa a Najeriya.

A baya, rahotanni sun nuna danganta matsalar da gurbataccen man da aka shigo da shi da kuma rashin hanya saboda ambaliyar ruwa, da dai sauransu.

Shin me ya sa wahalar man ta ki karewa duk kuwa da cewa an shawo kan wadancan mastalolin da aka dora wa laifin a baya?

Shirin Najeriya A Yau, ya tattauna da masu ruwa da tsaki da masana kan al’amarin da kuma mafita.