Wata bakuwar cuta mai halaka kanana yara ta hanyar toshe musu maƙogwaro da ake kira da Diptheria a Turance, ta bulla a Jihar Kano, inda kawo yanzu rahotanni suka bayyana mutuwar yara 25 a unguwanni biyu a cikin kamar Hukumar Ungogo da ke Jihar.
Shin wace cuta ce wannan?
Shirin Najeriya A yau ya bibiyi labarin cutar, ya kuma ji ta bakin masana kan abin da ya kamata a yi.