A jiya Alhamis, 26 ga watan Janairun 2023 aka gudanar da Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 20 a Abuja, babban birnin Najeriya. Taron, mai taken: Bibiyar Manufofin ’Yan Takarar Shugaban Kasa a 2023 ya gudana ne a Dakin Taro na Cibiyar Sojin Saman Najeriya da ke Abuja, wato NAF Center.
Shin kun san manufofin ’yan takarar shugabancin kasa da aka bibiya?
Shirin Najeriya A Yau ya bibiyi wannan taro, ya kuma ji ta bakin masu sharhi kan al’amuran yau da kullum.